6 Sep, 2026

Sojojin Nijeriya sun ceto mutum 36 da aka sace a kasar, sun kuma halaka ’yanta’adda da dama

Sojojin sun ce sun halaka wasu manyan kwamandojin ’yanta’adda guda biyu tare da jikkata wani na uku yayin wani samame da suka kai kan wasu maɓoyar ’yanta’adda da ake zargi a Kogo da ke Matazu, Jihar Katsina, a ranar 31 ga Agusta

5ceeac3e 993c 4f1b 838b cdce54833a51 1788676415474

5 Sep, 2026

‘Yanbindiga sun kashe mutum biyar tare da jikkata uku a wasu ƙauyukan Sokoto

Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da aka ruwaito cewa ‘yanbindiga sun sanya wa garin Kebbe harajin naira miliyan 40 a yammacin ranar Talata, lamarin da ke ƙara nuna irin matsin lambar da al’ummomin ƙaramar hukumar ke fuskanta.

1c7a8d8c da30 4acd b380 33baf1580bd8 1788589753137

4 Sep, 2026

Darakta Janar na DSS ya umarci jami’ansu da kar su kama kowa yayin da farar-hula suka samu sabani

Adeola Ajayi, darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke Nijeriya ya umarci jami’ansu da kar su kama kowa idan aka samu sabani a tsakanin ‘yan kasar.

709e229d 9c78 4956 87c6 71816cb07bd6 1784621914045

4 Sep, 2026

Nijeriya ta musanta zargin goyon bayan yunƙurin ‘juyin mulki’ a Nijar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai cewa an ƙirƙire su ne domin bata sunan Nijeriya da kuma haddasa rarrabuwar kawuna.

1f6566b7 4e2f 4996 b754 cae07ca07009 1788501118461

3 Sep, 2026

Hukumar DSS ta Nijeriya ta ƙwato bindigogi 676 da harsasai 332,000

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya ta ce ta kwato bindigogi 676 na zamani da kuma harsasai fiye da 332,000, a wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi na daƙile hanyoyin samar da makamai ga ‘yanta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a ƙasar.

709e229d 9c78 4956 87c6 71816cb07bd6 1784621914045

3 Sep, 2026

INEC za ta yi zaɓen gwaji na Shugaban Ƙasa gabannin zaɓen 2027 na Nijeriya

Ya yi kira da a haɗa fasahar zaɓe da ta sadarwa a wuri ɗaya gabannin zaɓen 2027, yana mai gargaɗin cewa labaran ƙarya da aka kitsa da ƙirƙirarriyar basira na gagarumar barazana ga sahihancin zaɓukan.

db7d9e1f 638b 4a23 a658 65c202e4335e 1776676291004

3 Sep, 2026

An lalata makarantu fiye da 1000, an kashe malamai 2,295 a Arewa maso Gabashin Nijeriya – Hukumomi

Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya ce alƙaluman sun nuna mummunan tasirin da matsalar ta’addanci ta tsawo lokaci ta yi ga yara, musamman kan lafiyar ƙwaƙwalwarsu da iliminsu da kuma makomarsu a gaba.

eebfa1ed bc1e 48ea b847 cafa83eb8e66 1780654028396

2 Sep, 2026

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kashe ‘yanta’adda 1,500 da kubutar da mutane 777 a watanni biyu

A wasu farmakan soji da suka kai, dakarun Nijeriya sun hallaka ‘yanta’adda 1,487, tare da kubutar da mutane 777 da aka yi garkuwa da su a watannin Yuli da Agusta, in ji Hedikwatar Tsaron ƙasar a ranar Talata.

0849398a 8e23 4602 b2b9 123051bcc057 1786463870154

1 Sep, 2026

EFCC ta kori ma’aikatanta fiye da 40 saboda zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin yayin wani taro da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yanjarida.

3b4444dd 3823 4cdc 9627 586f67ab6f0a 1788262703149

1 Sep, 2026

Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan ceto masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su

Mutanen da aka ceto suna samun kulawa ta lafiya kafin daga bisani a hada su da iyalansu,” in ji sakon shugaban.

87eeb304 227e 4f6d 8c08 b10a681a7a4d 1788243443356
Ana lodawa...