24 Aug, 2026

Dawo da tallafin fetur zai mayar da Nijeriya baya a cigaban tattalin arzikinta — Minista

Ministan watsa labaran Nijeriya Mohammed Idris ya ce mayar da tallafin zai kusan mayar da Nijeriya nan take zuwa yanayin tattalin arzikin shekarar 2022, tare da sake haifar da matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati.

ccc5bfae 5583 49b5 98c7 9030e2b83fe1 1787585695174

24 Aug, 2026

Wani bidiyo ya nuna mutum 600 da aka yi garkuwa da su a wani harin masallaci a jihar Neja a Nijeriya

Wani bidiyo ya nuna mutane kimanin 600 da aka yi garkuwa da su a wani harin masallaci a jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga mazauna yankin.

902b7796 ed94 433c a55b 63ca937dfc48 1780653962415

24 Aug, 2026

NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101 da tabar wiwi a cikin garin alabo

A cewar NDLEA, matar mai shekaru fiye da 100 ta shaida wa masu bincike cewa ta shiga harkar sayar da miyagun kwayoyi baya gobara ta lalata shagonta na da take sayar da kayan abinci.

64fcd99b a145 4a27 bdd5 e16eb0b49c4f 1787558673541

23 Aug, 2026

Dakarun Nijeriya sun kashe fiye da ‘yanta’adda 20 a samamen da suka kai Borno

Hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai mai yaƙar ‘yanta’adda a arewa maso gabashin ƙasar ta ce hare-haren saman sun kassara taron ‘yanta’addan tare da hana su zirga-zirga a yankin.

58920d7b 0fac 4afb 8012 ec590e041eae 1783844975711

23 Aug, 2026

Za mu tabbatar Tinubu ya lashe zaɓen Nijeriya na 2027— Abdulaziz Yari

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya yi wannan alƙawarin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar yayin da yake gode wa Tinubu da jam’iyyar bisa yarda da suka yi da shi.

49d99eb3 addf 4384 bfbf 07cd7be00157 1787468832545

22 Aug, 2026

Tinubu ya buƙaci ‘yanmajalisar yaƙin neman zaɓensa su bayyana wa ‘yan Nijeriya nasarorin gwamnatinsa

Shugaban ya buƙaci waɗanda aka bai wa muƙamai a cikin majalisar su tuntuɓi ‘yan jam’iyar waɗanda ba a saka sunayensu a cikin jerin sunayen waɗanda aka naɗa ba su taya su aiki.

5af7cbc4 556c 47db bc8a 3990ce260fa2 1779683525526

21 Aug, 2026

Tinubu ya yi umarnin kama wani mutum, ya dakatar da manyan sakatarori bayan gano wata hukuma ta bogi

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) Dokta Musa Adamu Aliyu, SAN ya ce an bai wa sabuwar hukumar ta bogi da aka gano ofishi ba bisa ƙa’ida ba a harabar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

eae9745e 2160 4c1f 9abd e1d1c48c157e 1786003471953

21 Aug, 2026

Iyalai sun yi zanga-zanga a Nijeriya kan yaran da aka sace kusan kwanaki 100 da suka gabata

An sace yaran ne daga ajujuwansu ranar 15 ga watan Mayu a Mussa, wani gari da ke kusa da Dajin Sambisa, wajen da ‘yanta’addan Boko Haram suka daɗe suna da ƙarfi a ciki.

b5a4a72d 7987 4c30 8e31 fa78c64130bf 1787237343346

21 Aug, 2026

EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da Maryam Shehu da Abubakar Shuraim kan zargin ɓata suna

Sakin nasu ya zo ne a daidai lokacin da lauyoyin Maryam suka shigar da buƙatar bayar da belinta don samun damar rubuta jarrabawar shekarar karshe a jami’a, kamar yadda ɗaya daga cikin lauyoyin Abba Hikima ya bayyana a shafinsa na Facebook.

ae94d26e ae67 407b b0b5 1b85e73ce099 1787323248826 main 1

21 Aug, 2026

Kira a mayar da tallafin fetur jahilci ne kan yadda ake tafiyar da tattalin arziki – Tinubu

Martanin Tinubu ya zo ne kwana guda bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wata hira inda ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027.

13604e37 0529 4adb a00d 1aa9aa39acff 1787300367716
Ana lodawa...