Wasanni

Onana ya yi murna da kuri bayan barin Manchester United zuwa Trabzonspor ta Turkiyya

Tsohon golan Manchester United, Andre Onana ya ce bai taɓa ganin soyayyar da ya gani a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya ba, inda ya koma aro a makon nan.

Newstimehub

Newstimehub

12 Sep, 2025

f16fa94bfa58762ee3d0ab5d9b469f5400157cdc202707cbc3accc15f07e12c3

Andre Onana, tsohon golan Manchester United ya ce bai taɓa ganin soyayyar da ya gani a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya ba, inda ya koma aro a makon nan.

Onana ya kammala komawa Trabzonspor aro bayan da aka tilasta masa barin Man U, inda aka rage masa daraja a zaɓar masu buga wasa ƙarƙashin koci Ruben Amorim.

Ɗan asalin Kamaru, Onana ya je United ne a 2023 kan kuɗi fam miliyan 47.2.

A yanzu zai nemi farfaɗo da tagomashinsa a gasar Super Lig ta Turkiyya, inda ya bayyana tsananin farin cikinsa da yadda ya samu tarba a Turkiyya.

A maraicen Alhamis ne Manchester United ta tabbatar da ƙaurar Onana mai shekaru 29 zuwa Trabzonspor a matsayin aro na tsawon kakar 2025-26.

Kocin United ya zaɓi yin aiki tare da golansa na biyu Altay Bayindir, kafin daga bisani ya sayo wani golan, Lammens kan fam miliyan 18.2.

Kurarin Onana