Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi gargadi cewa amfani da hanyoyin sadarwa da ba su karkashin ikon gwamnatin Rasha ba a fagen daga na iya jefa sojoji cikin hadari. Ya bayyana hakan ne a Moscow yayin wata ganawa da mata sojoji gabanin bikin Ranar Mata ta Duniya.
A yayin tattaunawar, Putin ya yi magana da wata jami’ar sadarwa ta soja, Irina Godunova, wadda ta ce ana amfani da manhajar Telegram a fagen daga, amma ta bayyana ta a matsayin hanyar sadarwa ta abokan gaba. Ta kuma jaddada bukatar samar da karin tsarin sadarwa na cikin gida da Rasha za ta iya sarrafawa da kanta.
Putin ya kuma ambaci batun katse amfani da tsarin intanet na Starlink ga masu amfani da shi a Rasha, yana mai cewa abokan gaba na ci gaba da amfani da irin wadannan hanyoyi na kasashen waje yayin da sojojin Rasha ke fuskantar takurawa wajen amfani da su.
Tun daga shekarar 2019, hukumomin Rasha ke takaita amfani da wasu manyan manhajojin sada zumunta da na sadarwa kamar Facebook, Instagram, LinkedIn, YouTube da WhatsApp. Haka kuma an taba takaita Telegram a farkon watan Fabrairu, sai dai daga baya aka janye takunkumin bayan korafe-korafen da sojoji suka gabatar.













