Wani rahoto da jaridar New York Times ta fitar ya bayyana cewa gwamnatin Donald Trump ta kora wasu mutane tara zuwa ƙasar Cameroon ba tare da cikakken sanarwa ba. Abin da ya fi ba mutane mamaki shi ne cewa wasu daga cikin waɗanda aka korar na da kariya daga kotunan Amurka.
Rahoton ya kuma nuna cewa babu ko ɗaya daga cikinsu da ya fito daga Cameroon, lamarin da ya ƙara jawo tambayoyi da cece-kuce kan yadda aka bi doka da kuma tsarin shari’a. Wannan mataki ya tayar da muhawara a tsakanin masu sharhi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
Jaridar ta ce wasu daga cikin mutanen ba su san inda ake kai su ba sai bayan an saka su a jirgin Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida (DHS) daga Alexandria, Louisiana, a ranar 14 ga Janairu. An ruwaito cewa an ɗaure su da ankwa da sarƙoƙi kafin tashin jirgin.
Hukumar DHS, Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Cameroon ba su fitar da martani nan take ba. Haka kuma, babu wata yarjejeniya da aka sanar a hukumance da ke nuna cewa Cameroon ta amince da karɓar ‘yan ƙasashen waje da aka kora daga Amurka.
Lamarin ya sake tayar da muhawara kan manufofin shige da fice da kuma yadda ake aiwatar da korar mutane, musamman ma ga waɗanda ke da kariyar doka.
Majiyar Labari: TRT WORLD














