Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles, na fafatawa da Taifa Stars ta Tanzania a wasansu na farko a Rukunin C na gasar Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) ta 2025. Bayan gaza tsallakewa zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026, Nijeriya na neman fansa, inda ta fara da wasan da Tanzania.
67′: Osimhen ya karɓi ƙwallo mai kyau a tsakiya, amma bugunsa bai isa ya doke mai tsaron gida ba.
59′: Sauye-sauye a ɓangaren Super Eagles: Dele-Bashiru da Moses Simon sun maye gurbin Samuel Chukwueze da Akor Adams.
52′: Nijeriya ta koma gaba bayan Ademola Lookman ya zura ƙwallo mai ƙarfi daga wajen akwatin bugun fanareti!
50′: Tanzania ta rama da sauri bayan kammala wata kyakkyawar dama.
46′: Babu sauyi a ɓangaren Nijeriya. Osimhen ya zura ƙwallo amma alƙalin wasa ya soke ta saboda offside.
45′: An tashi daga zagaye na farko da Nijeriya na gaba da ci 1-0 a birnin Fes.
37′: Super Eagles sun fara cin ƙwallo! Semi Ajayi ya kai ƙwallon da Alex Iwobi ya tsallaka masa kai tsaye cikin raga, Nijeriya ta ja da ci 1-0.
35′: Victor Osimhen ya doke mai tsaron gida, amma an fitar da ƙwallon daga layin raga.
30′: An shafe rabin sa’a ana wasa, Nijeriya ce ke rinjaye, amma har yanzu babu ƙwallo ta biyu.
20′: Duk da matsin lamba da Nijeriya ke yi tun farko, har yanzu ba su samu ƙwallo ba.
13′: Tanzania ta kai hari, amma bugun acrobatic ɗin bai wahalar da Stanley Nwabali mai tsaron ragar Nijeriya ba.
10′: Akor Adams ya buga ƙwallo ta bugi sandar raga daga bugun kusurwa, Taifa Stars suka ɗan numfasa.
09′: Akor Adams ya kusa cin ƙwallo, amma mai tsaron gida ya hana shi; ana duba lafiyarsa.
05′: Samuel Chukwueze ya buga ƙwallo kai tsaye zuwa ga mai tsaron ragar Tanzania, yayin da Tanzania ke karewa sosai.
02′: Zaidu Sanusi ya tura ƙwallo cikin akwatin bugun fanareti, amma babu wanda ya haɗu da ita.
01′: An fara wasan!














