Sabon tashin hankali da ya ɓarke a Sudan ta Kudu ya jefa dubban fararen hula cikin firgici, inda ake ci gaba da jin karar harbe-harbe da fashewar bama-bamai a wasu yankuna. Mutane na tserewa daga gidajensu zuwa dazuzzuka da wuraren da suka fi ganin aminci, domin tsira da rayukansu daga mummunan rikicin da ke ƙara tsananta.
A cewar rahotannin Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA), fiye da mutane 180,000 ne aka raba da muhallansu a jihohi huɗu na jihar Jonglei, bayan sabbin faɗace-faɗace tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan adawa. Shaidu sun ce an yi artabu mai tsanani a yankin Duk, inda aka yi amfani da manyan makamai, lamarin da ya tilasta wa al’umma tserewa zuwa kurmi.
Wani mazaunin yankin, Daniel Deng mai shekara 35, ya ce ya rasa komai sakamakon rikicin. “Ba ni da inda zan dosa sai daji, domin a can ne kawai na ke ganin rayuwa za ta fi aminci,” in ji shi.
Rikicin ya ƙara muni ne bayan da aka kama Mataimakin Shugaban Ƙasa Riek Machar a watan Maris, wanda ya janyo rikicewar yarjejeniyar raba madafun iko tsakaninsa da Shugaba Salva Kiir. Tun daga lokacin, artabu ya ƙara yawaita, musamman a watan Disamba a Jonglei.














