Rahotanni daga kafofin watsa labaran Libya sun bayyana cewa an kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, yana da shekaru 53. Lauyansa Khaled el-Zaydi da mai ba shi shawara Abdullah Osman sun tabbatar da mutuwarsa ranar Talata, inda rahotanni ke cewa an kai harin ne a gidansa bayan kashe na’urorin kyamarorin sa ido, tare da zargin wasu mutane huɗu da ba a san ko su wanene ba.
Ofishin babban lauyan Libya ya ce ya fara bincike kan lamarin, duk da cewa har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da cikakken bayani ba.
A wani sakon Facebook, Moussa Ibrahim, tsohon kakakin gwamnatin Gaddafi, ya bayyana kisan a matsayin “hai’inci” da nufin kara raba Libya da hana hadin kan kasa. Sai dai rundunar “Birged na 444” da ke da alaka da ma’aikatar tsaron gwamnatin hadin kan kasa ta musanta duk wata alaka da abin da aka yada.
Saif al-Islam, wanda aka kama bayan hambarar da gwamnatin mahaifinsa a 2011, ya dade yana zaune a Zintan kafin a sake shi a 2017, kuma tun daga lokacin ba a san takamaiman inda yake ba, lamarin da ya kara jefa labarin mutuwarsa cikin duhu a kasar Libya.
Majiyar Labari: TRT AFRIKA














