Kwallon fenariti da Mohamed Salah ya ci ta bai wa Masar nasara a kan Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta tsallaka zuwa zagaye na gaba a gasar AFCON 2025.
Tawagar Masar ta doke Afirka ta Kudu da ci 1-0 a wasan da aka buga ranar Juma’a a Agadir, duk da cewa ta kammala wasan da ‘yan wasa 10. Kyaftin ɗin ƙungiyar, Mohamed Salah, ne ya zura kwallon nasara ta fenariti a minti na 45.
Masar ta rage da mutum ɗaya a ƙarshen hutun farko bayan an kori ɗan bayan dama, Mohamed Hany, sakamakon katin gargadi na biyu. Duk da haka, ‘yan Masar sun tsaya tsayin daka har suka kare nasarar.
Afirka ta Kudu ta nemi fenariti a rabin na biyu bayan da ake zargin Yasser Ibrahim ya taɓa ƙwallo da hannu a cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma alkalin wasa ya ƙi amincewa.
Bayan wasanni biyu a Rukunin B, Masar – wadda ta lashe AFCON sau bakwai – ta samu maki shida, abin da ya tabbatar mata da matsayi na biyu aƙalla da kuma tikitin zuwa zagaye na 16. Afirka ta Kudu na da maki uku, yayin da Angola da Zimbabwe ke da maki ɗaya-biyu bayan canjaras dinsu.
Mai tsaron ragar Masar, Mohamed El Shenawy, ya taka muhimmiyar rawa a wasan, inda ya hana Afirka ta Kudu damar cin kwallo sau da dama a rabin na biyu, musamman bayan da suka samu rinjayen yawan ‘yan wasa.
Majiyar Labari: TRT WORLD














