Sanatocin Amurka sun bayyana matsananciyar damuwa kan halin tsaro da na jin ƙai a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), yayin wata ganawa da Shugaba Felix Tshisekedi a Washington. Sun ce halin da yankin ke ciki ya wuce a yi shiru a kai, musamman ganin yadda fararen hula ke ci gaba da shan wahala sakamakon rikice-rikicen da ba su ƙare ba.
A cewar sanarwar, sanatocin sun nuna fargaba kan ci gaba da mamayar wasu sassan gabashin Congo da ƙungiyar ’yan tawaye ta M23 ke yi, wadda Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen Yamma ke zargin tana samun goyon bayan Rwanda—zargin da Rwanda ta musanta. Sun kuma bayyana halin jin ƙai a yankin a matsayin abin da ba za a iya ɗauka ba, inda mutane kusan miliyan 26 ke fuskantar matsanancin ƙarancin abinci.
Jawaban sun fito ne daga Jim Risch da Jeanne Shaheen, shugabanni a Kwamitin Harkokin Wajen Majalisar Dattawan Amurka, sa’o’i kaɗan bayan wata ƙungiya mai suna Congo River Alliance, wadda ta haɗa da mayaƙan M23, ta ɗauki alhakin harin da aka kai filin jirgin saman Kisangani Bangoka a makon jiya. Rahotanni sun ce M23 na iko da manyan yankuna a gabashin Congo, ciki har da biranen Goma da Bukavu, da aka ƙwace a farkon 2025.
Tattaunawar da aka yi a Majalisar Dokokin Amurka ta mayar da hankali kan yarjejeniyar Washington Accords for Peace and Prosperity, da kuma makomar alaƙar Amurka da DR Congo. Sanatocin sun ce dole ne sojojin Rwanda su fice daga yankin idan ana son samun zaman lafiya mai ɗorewa. Sun kuma jaddada cewa mata, yara da ƙananan al’ummomi ba za su ci gaba da zama abin da rikici ke lalata ba.
Haka kuma, tattaunawar ta shafi haɗin gwiwa kan ma’adinai masu muhimmanci da saka hannun jari a Lobito Corridor, domin bunƙasa kasuwanci da haɗin kai tsakanin Amurka da Afirka. A ƙarshe, sanatocin sun bukaci gwamnati a Kinshasa da ta ɗauki matakai masu ƙarfi kan ’yan tawayen FDLR da kuma ’yan sa-kai na Wazalendo, domin rage tashin hankali da kare al’ummomin yankin.
Majiyar Labai: TRT AFRIKA














