Duk da rikicin siyasa da ya ɓarke kwanan nan kan halin da ake ciki a Yemen, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun kammala wani atisayen soja na haɗin gwiwa, lamarin da ke nuna ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan tsaro a yankin Gulf.
Ma’aikatar tsaron UAE ta bayyana cewa atisayen mai suna “Garkuwar Gulf 2026” ya gudana ne a Saudiyya, tare da halartar rundunonin sama da na kariyar sararin samaniya na ƙasashen Majalisar Haɗin Kan Gulf (CCG), da kuma rundunar soja ta haɗin gwiwa ta CCG.
Ƙasashen CCG guda shida sun haɗa da Saudiyya, UAE, Bahrain, Qatar, Kuwait da Oman.
A nata ɓangaren, ma’aikatar tsaron Saudiyya ta ce atisayen na daga cikin matakan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a yankin, da kuma haɓaka shirin yaƙi da haɗin kai tsakanin rundunonin Gulf. Atisayen ya haɗa da kwaikwayon barazanar jiragen sama da makaman linzami, da atisayen jiragen yaƙi na haɗin gwiwa.
Sai dai wannan atisaye ya zo ne a daidai lokacin da aka samu sabani mai tsanani tsakanin Riyadh da Abu Dhabi kan Yemen. A ƙarshen Disamba, Saudiyya ta zargi UAE da goyon bayan ƙungiyar Southern Transitional Council a yankunan Hadramaut da Al-Mahra.
UAE ta musanta zargin, tana mai cewa kayan yaƙin da aka ambata na sojojinta ne kawai, kafin daga bisani ta sanar da janye ragowar dakarunta daga Yemen. A halin yanzu, dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan Saudiyya sun sake karɓe iko da Hadramaut da Al-Mahra.
Batun rabuwar Arewa da Kudancin Yemen, duk da haɗewar ƙasar a 1990, na ci gaba da zama babban tushen rikici da rashin zaman lafiya a ƙasar.














