Wasanni

Senegal za ta daukaka ƙara kan hukuncin ƙwace mata Kofin AFCON 2025

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta ce za ta ɗaukaka ƙara “cikin sauri” zuwa Kotun Sulhu Kan Wasanni ta Duniya, bayan da aka karɓe mata kofin AFCON 2025 da ta lashe, kuma aka bai wa Maroko.

Newstimehub

Newstimehub

18 Mar, 2026

aa8a7c490148afd6f18c5334fc3a3663dc360b05361424f1265f870f56c684a0

Senegal ta ce za ta ɗaukaka ƙara bayan da aka kwance mata kambin Gasar Kofin Ƙasashen Afirka a ranar Talata, inda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF ta bayyana Maroko a matsayin zakara, watanni biyu bayan wasan ƙarshe da ya zo da ruɗani.

Wasu ‘yan wasan Senegal da dama sun bar filin wasa a Rabat, lokacin wasan ƙarshe ranar 18 ga Janairu don nuna adawa lokacin da aka ba masu masaukin baƙi, Maroko bugun ɗurme a nintunan ƙarshe na ƙarin lokaci.

A ƙarshe ‘yan wasan Senegal sun dawo fili, bayan da kyaftin ɗin tawagar, Sadio Mané ya shawo kan su. Maroko ta ɓarar da fanaretin sannan daga bisani Pape Gueye ya zura ƙwallo a ragar Maroko a ƙarin lokaci, wanda ya ba Senegal nasara da ci 1-0.

CAF ta ce bayan ta yi nazari kan ɗaukakar ƙorafin Maroko, “an ayyana cewa tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta yi watsi da wasan”, kuma an yanke sakamakon wasan a hukumance a matsayin ci 3-0 nasara ga Maroko.

Kwamitin ɗaukaka ƙarar CAF ya bayyana dalilin wannan hukunci ta amfani da Dokar AFCON, Saɗara ta 82 da 84, waɗanda ke cewa idan wata ƙungiya “ta ƙi yin wasa ko ta bar fili kafin ƙarshen wasa na al’ada, ba tare da izinin alƙalin wasa ba, za a ɗauke ta a matsayin ta yi rashin nasara kuma za a kore ta daga wannan gasar gabaɗaya”.

Ƙa’idojin gasa

Dokokin gasar sun ƙara da cewa, ƙungiyar da ta karya waɗannan ƙa’idoji “za ta rasa nasara a wasan ta da ci 3-0”.

A cikin wata sanarwa, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Maroko (FRMF) ta ce ɗaukakar ƙararta “ba ta nufin ƙalubalantar ƙwarewar wasanni na ƙungiyoyin da suka halarci gasar, sai dai neman a aiwatar da ƙa’idodin gasar kawai”.

“Hukumar ta sake tabbatar da aniyarta ta girmama dokoki, da bayyana tsarin gasa, da kuma tabbatar da amincin a gasannin Afirka,” in ji sanarwar.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta ce za ta ɗaukaka ƙara “da zarar ta samu dama” zuwa Ƙotun Sulhu kan Wasanni (Court of Arbitration for Sport).

“Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta yi tir da wannan hukunci mara adalci, wanda ba a taɓa gani ba kuma ba za a iya karɓa ba, wanda ya ɓata sunan ƙwallon ƙafa a Afirka,” in ji hukumar a cikin wata sanarwa.

Ruɗani a filin wasa

Mintuna kaɗan kafin ƙarshen wasan, wasu magoya bayan Senegal sun yi ƙoƙarin shiga cikin filin wasa, yayin da ‘yan wasan Senegal suka dakatar da wasan kusan mintuna 20, domin nuna rashin amincewa da fanaretin da aka ba Maroko a ƙarshen wasa.

Alƙalin wasa ɗan asalin Congo DR, Jean-Jacques Ndala ya ba da wannan bugun fanareti mai jayayya, ana ƙarshen ƙarin mintuna takwas da aka bayar bayan, sakamkon duba bidiyon VAR kan tarewa da El Hadji Malick Diouf ya yi wa Brahim Díaz.

A lokacin, babu wanda ya ci ƙwallo, kuma Díaz zai iya ba wa Maroko kofin da wannan fanareti a minti na 24 na ƙarin lokaci kuma a ƙarshen lokacin wasa na al’ada.

Amma mai tsaron ragar Senegal, Édouard Mendy, ya tare bugun ‘Panenka’ da Diaz ya yi ƙoƙarin yi, wanda ake ganin ya samu shagala saboda dogon jinkirin da ya biyo bayan bayar da bugun.

Wasan da aka buga a filin wasa na Prince Moulay Abdellah ya kai ga ƙarin lokaci, inda Pape Gueye ya zura ƙwallo a minti na 94, wanda ya ba Senegal nasara.

Martanin ‘yanwasa

Bayan sanarwar cewa an ƙwace musu kofin, wasu daga ‘yan wasan Sengal sun wallafa saƙonni a kafafen sada zumunta.

Ɗanwasan baya, Moussa Niakhaté, mai buga wasa a kulob ɗin Lyon na Faransa, ya saka hotonsa yana ɗaga kofin AFCON tare da saƙon da ya ce “sun yi hauka”, a abin da ake ɗauka yana nufin CAF.

A lokacin kammala wasan ƙarshen, shugaban FIFA Gianni Infantino ya yi tir da “wasu ‘yanwasan Senegal” saboda “mummunar halayya”.

“Ba daidai ba ne a bar filin wasa ta irin wannan halin, kuma ba za a lamunci tashin hankali a wasanninmu ba, wannan ba daidai ba ne,” in ji Infantino, wanda ya halarci wasan.

A ƙarshen Janairu, CAF ta ɗora jerin hukuncin ladabtarwa, ciki har da tara da ta kai dubunnan euro, ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashen biyu saboda rashin ɗa’a a wasa da kuma taka ƙa’idodin nuna adalci a wasa.

An tsare magoya bayan Sengal su 18 tun lokacin wasan ƙarshen, kuma aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsakanin watanni uku zuwa shekara ɗaya kan zargin “dabanci”.

A yanzu a ɗage sauraron ɗaukakar ƙara kan magoya bayan Senegal ɗin, wadda aka shirya yi a ranar Litinin mai zuwa, zuwa 30 ga Maris.