Turkiyya

Recep Tayyip Erdogan Ya Aika Sakon Ramadan Ga Al’ummar Turkey Da Duniya

Shugaban Turkiyya ya yi fatan watan Ramadan zai kawo albarka, rahama da karfafa hadin kai ga Musulmi da dukkan bil’adama.

Newstimehub

Newstimehub

19 Feb, 2026

1094e3ff86874d6a2ca08ae4f590cb2b5f5c9366675afaf2ebfe5db862616c13

Yayin da watan Ramadan ya fara, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya mika sakon taya murna ga al’ummar Turkiyya da duniyar Musulmi, yana mai rokon watan ya zo da zaman lafiya da hadin kai.

A sakonsa da ya wallafa a shafin sadarwa na NSosyal, Erdogan ya bayyana Ramadan a matsayin wata dama ta bude kofofin rahama da gafara. Ya ce yana fatan watan mai alfarma zai kawo alherai ga kasarsa, duniyar Musulunci da ma dukkan bil’adama.

Shugaban ya kuma yi addu’ar cewa kwanakin Ramadan za su zama sanadin karfafa zumunci, hadin kai da zaman tare a tsakanin al’umma.

Majiyar Labari: TRT HAUSA