Iran da Amurka sun fara nuna alamun ci-gaba a tattaunawar nukiliya da ake yi a kaikaice tare da taimakon ƙasashen yankin. Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana hakan ranar Lahadi, yana mai cewa tattaunawa ita ce hanyar da ƙasarsa ke bi domin cimma mafita ta lumana.
A wani sako da ya wallafa a shafin X, Pezeshkian ya jaddada cewa manufar Iran kan batun nukiliya ta dogara ne kan haƙƙin da aka tanada a yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya (NPT). Ya ƙara da cewa Iran na mayar da martani ga mutunci da ladabi, amma ba za ta amince da matsin lamba ko kalaman tilastawa ba.
Tattaunawar ta fara ne ranar Juma’a bayan makonni na tashin hankali, musamman bayan barazanar ɗaukar matakin soja daga Shugaban Amurka, Donald Trump. Duk da yanayin rashin aminci, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana tattaunawar a matsayin “mafari mai kyau,” yana mai cewa akwai yiwuwar ci gaba idan aka rage shakku tsakanin ɓangarorin biyu.
Araghchi ya kuma ce an amince a ci gaba da tattaunawar tare da sake ganawa a Muscat, Oman, nan gaba. Sai dai ya fayyace cewa shirin makami mai linzamin Iran ba ya cikin batun tattaunawa a yanzu ko a nan gaba, yana mai kiran shi “harkar tsaro” ta ƙasa.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














