Turkiyya

Shugaban Turkiyya ya yi wa Firaiministan Libya ta’aziyya kan rasuwar Babban Hafsan Sojojin ƙasar

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi wa Firaiministan Libya ta’aziyya bayan hatsarin jirgin sama a Ankara da ya kashe Babban Hafsan Sojojin Libya da wasu jami’ai.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

6b189c1da731ba2f77bc4689d0e77bf7035f18fe0534470683202d2f7ee6e030 e1766605470763

Cikin yanayin alhini, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya miƙa ta’aziyyarsa ga Firaiministan Libya, Abdul Hamid Dbeibah, bayan hatsarin jirgin sama a Turkiyya da ya yi sanadiyyar mutuwar Babban Hafsan Sojojin Libya da wasu jami’ai, lamarin da ya girgiza gwamnatocin ƙasashen biyu.

A cewar Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Burhanettin Duran, Shugaba Erdoğan ya tattauna da Dbeibah ta wayar tarho a ranar Laraba, inda ya bayyana baƙin cikinsa da jajantawa kan rasuwar Babban Hafsan Sojojin Libya, Janar Mohammed Ali Al-Haddad, da sauran mutanen da ke cikin tawagarsa.

Tun da farko, Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya bayyana cewa an gano tarkacen jirgin ƙirar Falcon 50 da ya tashi daga filin jirgin Esenboga na Ankara zuwa Tripoli a ranar Talata, inda aka same shi kimanin kilomita biyu kudu da Kesikkavak a gundumar Haymana ta Ankara.

Yerlikaya ya ƙara da cewa an gano baƙin akwatin jirgin da kuma na’urar rikodin murya a safiyar ranar Laraba, kuma an fara bincikensu domin gano musabbabin hatsarin.

Bayan faruwar lamarin, Gwamnatin Haɗin Kan Ƙasa ta Libya ta ayyana zaman makoki na ƙasa na kwanaki uku domin jimamin rasuwar manyan jami’an sojin ƙasar.

Majiyar Labari: Trt Hausa