Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun halaka ‘yan ta’adda da dama da suka fito daga tsaunukan Mandara na Jihar Borno

Sojojin Operation Hadin Kai sun dakile yunƙurin ’yan ta’adda na kai hari garin Bitta da ke Jihar Borno inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama da ƙwace musu makamai.

Newstimehub

Newstimehub

18 Dec, 2025

d4d93247b95a83c96589ef3d5f28017c771806869dc75e8e5f33fc67b7f6a099

Sojojin Operation HADIN KAI sun daƙile wani yunƙurin kai hari da ’yan ta’adda suka yi da sassafe daga tsaunukan Mandara domin kutsawa cikin Bitta, inda suka hallaka da dama daga cikin ’yan ta’addan tare da rage ƙarfin aikinsu sosai.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis, sojojin da ke samun tallafi daga na’urorin sa ido na zamani sun gano motsin ’yan ta’addan da ke tunkarar yankin. Cikin tsari, ƙwarewa da haƙuri na soja, sojojin suka ƙyale su domin kusantowa har zuwa nisan da ya dace kafin su buɗe wuta domin kare kansu.

Artabun ya kai ga hallaka da dama daga cikin ’yan ta’addan, ciki har da wani babban jagoran ‘yan ta’addan da mai ɗaukar bidiyonsa.

Yayin da sauran ’yan ta’addan da suka tsira suka yi ƙoƙarin ja da baya, sashen jiragen sama na OPHK ya kai hare-haren da suka dace da ƙwarewa, wanda ya ƙara tarwatsa waɗanda ke tserewa tare da katse hanyoyin gudunsu.

Bayan artabun, sojojin sun yi cikakken bincike tare da shawagi a yankin domin duba shi, lamarin da ya kai ga kwato muhimman kayan aiki da kayayyakin sufuri na ’yan ta’adda.

Abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da: na’urar ɗaukar bidiyo (camcorder), bindigogin AK-47, bel-bel na harsasai, wayar oba-oba, jigidar AK-47 guda 11 masu cike da harsasai, wayoyin salula guda 7, bindigogin PKT, jigiar harsasan bindigogin PKT da GPMG, da kuma babura da kekuna.

Ci gaba da bincike ya nuna alamun jinin a da ke bi a ƙasa da kuma kaburbura marasa zurfi, abin da ke nuna cewa ’yan ta’addan sun ƙara samun asarar rayuka a lokacin artabun da kuma hare-haren sama da suka biyo baya.

Bayan sojojin sun ci gaba da bin sawu, sun ga jinin ‘yan ta’addan a ƙasa, da kuma ƙaburburan da ba a gina yadda ya kamata ba a cikin dajin, waɗanda hakan duk alamu ne na wahalar da ‘yan ta’addan suka sha.