Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta ƙara zafafa hare-harenta kan ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabashin Nijeriya, inda ta halaka fiye da ‘yan ta’adda 35 a wani farmakin haɗin gwiwa da ta kai ta sama a kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru.
Hare-haren, waɗanda aka kaddamar da su da safiyar Asabar, 23 ga Agustan 2025, an aiwatar da su ne ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK), bayan wani yunƙurin kai hari da ‘yan ta’addan suka yi kan dakarun ƙasar a Kumshe da ke Jihar Borno.
Leƙen asiri daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa ‘yan ta’adda sun taru a wurare guda huɗu domin shirya kai farmaki. Sai cikin gaggawa Rundunar Sojin Saman Nijerya ta ƙaddamar da hare-hare cikin ƙwarewa da kan saiti a jere, inda hare-haren suka tarwatsa mayaƙan tare da daƙile harin da suka so kaiwa.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa daga baya sun yi magana da sojojin da ke ƙasa waɗanda suka tabbatar da cewa a wurin da suke komai na tafiya daidai bayan hare-hare ta sama da sojojin suka kai.














