Nijeriya

Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya gana da tsofaffin jami’an da suka yi zanga-zangar hakkokinsu

Tsofaffin ‘yan sandan sun yi zanga-zangar ne a ranar Litinin a Abuja, ƙarƙashin jagorancin wasu ‘yan fafutuka Omoyele Soware da Bello Galadanci da Deji Adeyanju da kuma Abba Hikima.

Newstimehub

Newstimehub

21 Jul, 2025

faa7e65ddee780271527d5ee99d22c42cbf02612fc3950df32af206848be541f

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya gana da tsofaffin  jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya da kansa, waɗanda suka yi zanga-zangar neman hakkokinsu.

Tsofaffin ‘yan sandan sun yi zanga-zangar ne a ranar Litinin a Abuja, ƙarƙashin jagorancin wasu ‘yan fafutuka Omoyele Soware da Bello Galadanci da Deji Adeyanju da kuma Abba Hikima.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a Facebook, ta ce Sufeto Janar din ya gana da jami’an ne a hedikwatar ‘yan sanda a Abuja, tana mai cewa “ganawar da IG ya yi da jami’an ta nuna irin ƙoƙarinsa na sauraron tsofaffin jami’an cikin mutuntawa.”

Sai dai rundunar ta ce ganawar ta ƙunshi sahihan tsofaffin ‘yan sandan ne waɗanda suka zaɓi tattaunawa a matsayin hanyar warware matsalarsu kawai.

Rundunar ba ta yi ƙarin bayani sosai ba kan matakan da Sufeto Janar ya ɗauka don magance koken tsofaffin ‘yan sandan.