A wani muhimmin mataki na gyaran fannin shari’a, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya roƙi Majalisar Dattawa da ta amince da ƙara yawan alkalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara da Babban Kotun Tarayya, domin rage cunkoson shari’o’i da ƙarfafa saurin yanke hukunci a faɗin ƙasar.
A wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta a zaman Talata, Tinubu ya nemi a gyara Dokar Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙara yawan alkalan daga 70 zuwa 110, sannan a yi wa Dokar Babban Kotun Tarayya kwaskwarima don ƙara alkalan daga 70 zuwa 90.
Shugaban ya kuma nemi tabbatar da naɗin Mai Shari’a Oyewole Joseph Kayode a matsayin Alkalin Kotun Koli, tare da gaggauta duba kudurorin da suka shafi kafa Cibiyar Magance Rikici (ADR) da kuma gyaran dokokin sashen lafiya 24.














