Tsohon kyaftin din tawagar ƙasar Kenya, Victor Wanyama, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 34. Wanyama, wanda ya shafe kusan shekaru 20 a harkar kwallo, ya zama tarihi a matsayin ɗan wasan Kenya na farko da ya taka leda a gasar English Premier League.
Ya koma Southampton FC daga Celtic FC a shekarar 2013 kan kusan fam miliyan 12.5. A can ya buga wasanni 85 tare da zura kwallaye hudu kafin daga bisani ya koma Tottenham Hotspur a 2016 kan kusan fam miliyan 11, inda ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa a tsakiya.

A sakon da ya wallafa, Wanyama ya bayyana tafiyarsa da cewa: daga yaro mai babban buri zuwa wakiltar kasarsa a manyan filayen duniya. Duk da cewa an taba kiransa ya dawo taka leda domin taimakawa tawagar kasa a karkashin koci Benni McCarthy a 2025, bai amince da hakan ba.
Majiyar Labari: AFRIKA NEWS














