Turkiyya

Turkiyya da Nijeriya Sun Ƙudiri Aniyar Ƙarfafa Kasuwanci, Zuba Jari da Tsaro

Sabbin yarjejeniyoyin na iya buɗe sabon babi na bunƙasar tattalin arziki da tsaro tsakanin Turkiyya da Nijeriya.

Newstimehub

Newstimehub

28 Jan, 2026

dde18e5684efc480b7e60bae2d77c3b850f00c6a49ffc8bfde05b638482affad

A wani mataki da ke nuna ƙara kusanci tsakanin Ankara da Abuja, Turkiyya da Nijeriya sun amince su ɗaga dangantakarsu zuwa sabon matsayi, ta hanyar zurfafa haɗin gwiwa a kasuwanci, masana’antu, zuba jari da tsaro, a yayin ziyarar aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai Turkiyya.

Ministan Ciniki na Turkiyya, Omer Bolat, ya ce ƙasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara, ciki har da kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Ciniki na Haɗin Gwiwa (JETCO), horon sojoji, tsaro, makamashi, ilimi, diflomasiyya, kafofin watsa labarai da harkokin halal, da nufin cim ma cinikayya ta dala biliyan biyar.

Cinikayya tsakanin ƙasashen biyu ta kai dala miliyan 688.4 a cikin watanni 11 na 2025, yayin da kamfanonin Turkiyya sama da 50 suka zuba jarin kusan dala miliyan 400 a Nijeriya, tare da ayyukan kwangila da darajarsu ta kusa kai dala biliyan 3. Haka kuma, haɗin gwiwar tsaro ya ƙaru, musamman bayan sayen jiragen yaƙi marasa matuki da jiragen helikwafta na Turkiyya da sojojin Nijeriya suka yi.

Majiyar Labari: TRT HAUSA