A wani yanayi da ke nuna ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tsaro tsakanin ƙasashen biyu, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a Ankara, inda ya jaddada cewa Turkiyya a shirye take ta ƙara haɗin-gwiwa da Nijeriya a fannonin horon soja, leƙen asiri da yaƙi da ta’addanci.
Erdogan ya bayyana cewa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, musamman a yankin Sahel, na zama babbar barazana ga zaman lafiyar Afirka, inda ya ce Ankara na duba hanyoyin ƙarfafa tallafi ga Nijeriya a wannan fanni. Haka kuma, shugabannin sun tattauna kan bunƙasa kasuwanci, makamashi, ilimi da masana’antar tsaro, tare da kudurin kai cinikayyar ƙasashen biyu dala biliyan biyar.
Shugaban Turkiyya ya nuna sha’awar ƙara zuba jari a fannin mai da iskar gas na Nijeriya, da kuma faɗaɗa haɗin gwiwa a ilimi, inda ya yaba da yawan ɗaliban Nijeriya da ke karatu a Turkiyya. Ziyarar ta Tinubu ta zo ne tare da tarba ta musamman ta faretin sojoji, alamar zurfafa dangantakar dabaru tsakanin Ankara da Abuja.














