Nijeriya

UNGA 80: Abubuwa biyar da Kashim Shettima ya faɗa a zauren MDD

Ya ce MDD za ta sake samun ƙimarta ne kawai idan ta nuna yadda duniya take a halin yanzu, ba yadda take a da can ba.

Newstimehub

Newstimehub

25 Sep, 2025

d1a2248b5a1da5525a65361e20b8b8dd7f4dd9ffb89eaee846d748da0c937674 main

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima ya yi jawabi a Babban Taron Majalisar rutsa da su ba wajen neman maslahar wasu. Mutane ne, waɗanda ƙimarsu ta yi daidai da tamu kuma sun cancanci irin ‘yanci da mutunci da dukkanmu muka saba da su,” in ji Shettima.

Yafe basussuka

Shettima ya ce duk da cewa Nijeriya da ma Afirka ta daidaita lamurra a cikin gida, suna buƙatar yafe basussuka.

“Muna buƙatar mataki na gaggawa domin yafe basussuka- ba wai a matsayin sadaka ba amma a wata hanya ga zaman lafiya da wadata da za ta amafani ga dukkanmu gabaɗaya,” in ji shi.

“Ina kira da a samar da wani sabon tsari da zai kuka da basusuukan ƙasashe, wani abu kaman kotun duniya na kuɗi, wanda zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar kuɓucewa daga tsarin tattain arziƙi na sayar da kayayyakin da ba a inganta ba,” a cewar Shettima.

Ya ce: “Muna buƙatar mataki na gaggawa na ƙarfafa yafe basusuuka da kuma samar da kuɗi.”

Amfana da ma’adinai

Daya daga cikin ababuwan da Shettima ya faɗa shi ne: “Ƙasashe masu arziƙin ma’adinai dole su amfana daga waɗannan ma’adinan.”

Ya ce tarihi ya nuna a Nijeriya cewa idan al’ummomin da ke inda ake samar da ma’adinai ba sa amfana da ma’adinan ba za a samun zaman lafiya ba.

“Saka jari wajen nema da inganta waɗannan ma’adinan a Afirka zai ruɓanya hanyar samar da ma’adinai ga kasuwar duniya da rage tashin hankali tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi.

“Zai kuma taimaka wajen tsara zaman lafiya da wadata a wata nahiyar da sau da yawa aka bari a baya yayin da ake tsere tsakanin ɓangarori,” in ji shi.

Ci-gaban ƙirƙirarriyar basira

Game da ƙirƙirarraiyar basira, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce fasahar tana tattare da ƙalubale mai yawa da ya kamata a magance su musamman ga ƙasashen Afirka.

“Dole mu cike giɓin ci-gaba na fasahar sadarwa. Kamar yadda abokinmu Babban Sakatare ya ce: dole ‘A.I.’ ya zaman wakilin ‘Afirka na Ciki’”, inji Shettima.

Ya ce ya kamata duniya ta yi amfani da damarmakin da fasaha ta samar da kuma samar da linzamin da ya kamata a samar masa domin inganta ci-gaba tare da hana ta’adin da zai iya haddasawa.

Ya ce abin ya da fi tayar masa da hankali shi ne matasa masu tasowa waɗanda ba su da yarda domin ba za su yarda da komai ba.