Duniya

‘Yan Afirka da suka je Indiya neman lafiya na cikin mutum 21 da gobarar hotal ta kashe a New Delhi

Firaministan India, Narendra Modi, ya ayyana bala’in da ya faru a matsayin “mai muni”, yayin da ayyukan ceto ke ci gaba.

Newstimehub

Newstimehub

3 Jun, 2026

aa4ec1e8 8966 43a6 b17c b9ea10170461 1780472786078

Aƙalla mutane 21 ne suka halaka lokacin da gobara ta mamaye wani hotal a New Delhi ranar Laraba, a wani lamari da ya zama ɗaya cikin mafi muni da aka gani a babban birnin na indiya.

Da dama cikin waɗanda suka rasu maziyarta ne daga ƙasashen Afirka waɗanda suka zo birnin neman lafiya, kamar yadda jaridar Indian Express da sauran jaridun yankin suka ambata.

Gobara a gine-gine na yawan abkuwa a India, saboda ƙarancin kayayyakin kashe gobara da kuma rashin bin dokokin kare rayuka.

Sanarwar ‘yansandan Delhi ta ce Gobarar ta fara ne da safiya a hotal ɗin Flourish Stay, wanda ke wata unguwa da ke da cunkoso a kudancin birnin.

“Muna baƙin cikin sanar da cewa mutum 21 sun mutu a wannan mummunan lamari,” cewar rundunar.

Aikin ceto

Sanarwar ta ce ana ci gaba da ayyukan ceto, inda aka kai fiye da mutum 40 zuwa asibitocin da ke kusa don samun kulawar lafiya.

A ƙarshe an ci ƙarfin gobarar da taimakon motocin kashe gobara takwas.

A wani saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na X, Firaministan India, Narendra Modi, ya ayyana bala’in da ya faru a matsayin “mai muni”, inda ya ce, “Ina miƙa gaisuwata ga makusantan waɗanda suka rasu”.

Hukumomi sun ƙaddamar da bincike don gano yadda gobarar ta samo asali da kuma batun ko rashin bin ƙa’idojin kariya ya taimaka wajen yawan mace-macen.

Ko a Maris ɗin da ya gabata, wata gobara a wani asibitin gwamnati a gabashin India ta halaka aƙalla mutum 10 majinyata.