Aƙalla mutane huɗu ne suka rasu bayan ’yan bindiga sun kai hari kauyen Damala da ke gundumar Woko a Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, da safiyar Asabar, 10 ga Janairu.
Harin ya faru ne mako guda kacal bayan wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a wasu ƙauyukan Borgu da Agwara, ciki har da kasuwar Daji da ke kauyen Demo.
Rundunar ’Yansandan Jihar Neja ta tabbatar da harin, inda kakakinta, SP Wasiu Abiodun, ya ce maharan sun afka ƙauyen, sun kashe mutane huɗu tare da sace shanu da kuma ƙona shaguna da dama kafin su tsere.
Ya ce jami’an tsaro sun gaggauta kai ɗauki zuwa yankin, tare da fara sintiri domin hana ƙarin hare-hare da kuma kamo masu aikata laifin.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.














