Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa fiye da ‘yan Nijeriya 67,000 a jihohi 25 ciki har da Babban Birnin Tarayyar ƙasar Abuja sun amfana da National Credit Guarantee Company (NCGC), wani shiri na musamman da gwamnatin tarayya ta tsara don sauƙaƙa wa ƙananan masana’antu ta hanyar ba su rance.
Tinubu ya bayyana wannan ci-gaban ne a jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, waɗanda ke zuwa a yayin da ƙasar ke shirin gudanar da bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Shugaban ya ce mutane 67,512 ne suka amfana da shirin a cikin shekara guda da ta wuce, ciki har da mata 11,374.
Ya ce kashi 33.5 cikin 100 na waɗanda suka ci gajiyar shirin ne suka fara samun rancen daga tsarin bankuna a karon farko.
NCGC tana bai wa bankuna tabbaci ko garantin biyan kusan kashi 60 cikin 100 na ragowar babban bashin idan mai karɓar ya kasa biya. Wannan yana ƙarfafa gwiwar bankuna su bayar da bashi ga kasuwancin da ba su da isasshiyar kadarar jingina.
A cewar shugaban, NCGC ya bayar da garanti na naira biliyan 21.59 kwatankwacin ($15.8 million) , wanda ya bai wa cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ke cikin shirin damar ba da rance naira biliyan 46.95.
‘‘Hakan na nufin duk naira ɗaya da aka bayar yana a matsayin garanti wanda ya taimaka wajen samar da kusan naira 2.17 na rancen,” in ji saƙon Tinubu a shafin X.
Shugaban ya ce fiye da ‘yan Nijeriya 22,000 sun samu damar shiga tsarin rancen banki a karon farko.
Ya ce biyan rance a kan lokaci zai taimaka wajen inganta tarihin rancen mutum, wanda zai iya sauƙaƙa samun ƙarin rance a nan gaba.
Rance ga ‘yan kasuwa da masu amfani
An kafa NCGC ne domin rage haɗarin da cibiyoyin kuɗi ke fuskanta wajen bayar da rance, tare da faɗaɗa damar samun kuɗi ga mutane da ‘yan kasuwa waɗanda ba su da isasshen kadarorin jingina ko tarihin rance.
A cewar Tinubu, NCGC a yanzu yana aiki tare da cibiyoyin hada-hadar kuɗi 19, ciki har da bankunan kasuwanci 13, da bankunan microfinance uku da cibiyoyin samar da kuɗaɗen raya tattalin arziki uku.
Shugaban ya ce ‘yan kasuwan da suka samu tallafin shirin suna da daidai da waɗanda suka samu guraben aikin yi kai tsaye da kuma a kaikaice guda 661,291.
Ya ba da misalin yadda samun rance zai bai wa ‘yan kasuwa damar ƙara yawan hajarsu, yayin da masana’antu za su iya faɗaɗa ayyukansu tare da samar da ƙarin guraben aikin yi.
An ƙaddamar da shirin rancen ne a watan Yulin 2026 karkashin Hukumar Kula da Rancen Masu Amfani ta Nijeriya (CREDICORP), tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Sadarwa, da Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani.
Shugaba Tinubu ya ce shirin na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka na mayar da Nijeriya zuwa tsarin tattalin arzikin da ya dogara da rance, tare da cika alkawarin da ya yi na inganta damar samun kuɗaɗen gudanar da harkokin kasuwanci.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da faɗaɗa damammakin samun rance a sassa daban-daban na ƙasar.

















