Waɗanda suka tsira daga wani bala’i a Nijeriya sun bayyana irin firgicin da suka shiga yayin da suke fama da wahalar numfashi a cikin ɗakin da aka tsare su, inda mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba suka mutu a lokacin da jami’an NSCDC suka tsare su.
’Yansanda sun yi harbe-harbe domin tarwatsa masu zanga-zanga, yayin da tashin hankalin ya bazu zuwa titunan Minna, babban birnin Jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya, wadda take da arzikin ma’adinai.
Ba a bayyana nan take ko ’yansandan na amfani da harsasan tarwatsa tarzoma ne ko kuma harsasai masu rai a Minna ba, inda gungun mutane suka tare wata babbar hanya tare da kai hari kan tashar sufuri, wani banki, ofisoshin jam’iyyun siyasa da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Gwamnati ta sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari domin daƙile tarzomar.
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da wani kwamandan rundunar tsaron fararen-hula, yayin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike “cikakke”, “na gaggawa” kuma “mai cikakken bayani da gaskiya” kan mutuwar da ta faru ranar Alhamis.
Sai dai al’umma sun fito sun nuna fushinsu a daidai lokacin da waɗanda suka tsira daga lamarin ke bayyana abubuwan da suka faru ke nuna cewa akwai yiwuwar mutanen da aka gwamutsa cikin ɗaki ɗaya ne ya jawo suka suƙe har suka rasu.
‘An yi biris da alamun mutuwa’
“Mun cika ɗakin tsarewar wanda ya cika maƙil, babu isasshen iska da za mu iya shaƙa,” kamar yadda Dauda Shehu ya shaida wa ’yan jarida a wani asibiti da ke cikin birnin.
“Nan take sai muka fahimci cewa ba za mu iya numfashi ba, kuma dukkanmu muka fara neman inda za mu samu iska mai kyau. Har sau da dama muka roƙe su, muka buga ƙofar ɗakin, amma suka ƙi amsa mana.
“Sau da yawa muna ta ƙara faɗakar da su cewa wasu mutane sun riga sun fara mutuwa saboda rashin iska, amma babu wanda ya amsa mana.”
Wani wanda ya tsira, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ya samu damar tsira ne saboda yana kusa da ƙofar ɗakin, inda yake iya samun iska sosai.
“Mun yi ta ihu muna neman taimako,” in ji shi, yana cewa ya gaya wa masu gadin cewa “mutane suna mutuwa ɗaya bayan ɗaya, amma ba su yarda da mu ba.”
Wani wanda ya tsira ya shaida wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, a gidansa cewa ɗakin da aka tsare su ya cika makil, kuma an umarce su da su tsaya a tsaye domin su samu damar shiga.
“Sun kulle ƙofar sannan suka fesa wani irin turare, kuma … wasu suka fara faɗuwa. Muka ci gaba da gaya musu cewa muna jin ƙishirwa, babu ruwa,” in ji shi da Hausa.
Iyalan waɗanda abin ya rutsa da su na neman adalci
Ya ce maƙogwaronsu da idanunsu sun riƙa ciwo. “Wasu daga cikinmu sun ci gaba da atishawa da tari.”
Wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 40 da aka wallafa a intanet, wanda aka ce yana nuna waɗanda abin ya rutsa da su a lamarin ranar Alhamis, ya nuna gawawwakin wasu da dama daga cikin samari sanye da gajerun wando kawai.
Yawancinsu sun bayyana kamar matasa ne, kuma gawawwakin sun warwatsu a ƙasa a fili.
Mallam Abdullahi ya rasa ɗansa, Salim, wanda ya ce shi ne mai ciyar da iyalin. Ya bayyana cewa ɗansa ya bar gida kwanaki uku kafin lamarin domin zuwa aikin haƙar ma’adinai, amma bai dawo ba.
“Su gaya mana ainihin abin da ya kashe ’ya’yanmu … Muna neman adalci,” Abdullahi ya shaida wa ’yan jarida.
“Kasancewar ana zargin waɗannan mutane da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ba ya kawar da ’yancinsu na rayuwa, mutunci da kuma samun kulawa irin ta ɗan Adam,” in ji Shugaba Tinubu.
“Ba za mu amince da mutuwar mutane sakamakon sakaci daga jami’an gwamnati, cin zarafi, rashin sauke nauyi ko kuma gazawar jami’an gwamnati wajen kare rayukan mutanen da aka ba su amanarsu ba.”

















