A wani mummunan lamari da ya girgiza al’ummar Jihar Kebbi, rundunar ’yan sanda ta cafke wani mutum mai suna Suleman Mamuda, mai shekara 30, bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, da fatanya a garin Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya bugi matarsa da fartanya har ta mutu, sannan ya tsere daga yankin domin kauce wa hukunci.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa bayan tserewar Mamuda, jami’an tsaro sun gudanar da bincike tare da samun sahihan bayanai daga al’umma, wanda ya kai ga gano inda yake da kuma cafke shi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya ba da umarnin mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.
Rundunar ’yan sandan Kebbi ta yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani lamari cikin gaggawa, tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka a fadin jihar.














