Nijeriya

‘Yanbindiga sun ƙone mutum 12 ‘yan gida ɗaya a Jihar Zamfara ta Nijeriya

Matar ƙanin Muhammadu Sani ce kawai ta tsira in ji rahotanni, yayin da sauran mutum 12 da ke cikin gidan sun mutu sakamakon tsananin zafi da wuta.

Newstimehub

Newstimehub

9 Nov, 2026

05c6521f cfa0 4bce 9be6 8c6993c4e49d 1794210249847

‘Yanbindiga sun kashe mutum goma sha biyu ‘yan gida ɗaya bayan sun cinna wa gidansu wuta a harin da suka kai wani ƙauye a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Kafofin watsa labaran ƙasar da suka haɗa da Daily Trust da The Punch da Premium Times da kuma Vanguard sun ba da rahoton cewa lamarin ya auku ne a ƙauyen Gidan Taba da ke Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara ranar Asabar da daddare.

Rahotanni sun ƙara da cewa an sace mutum bakwai a harin.

Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun far ma gidan wani mutum da ake kira Mallam Muhammadu Sani ne da misalin ƙarfe 10 na dare.

Mutum goma sha uku daga cikin gidan Muhammadu Sani, ciki har da matansa biyu da ‘ya’ya shida tare da matar ƙaninsa da ‘ya’yansu uku ne suka maƙale a cikin wani ɗaki bayan sun rufe kansu a ciki domin kuɓuce wa maharan don kada su yi garkuwa da su.

‘Yanbindigar sun umarci waɗanda suke cikin ɗakin su buɗe ƙofa, amma da suka ƙi, sai suka cinna wa ɗakin wuta, in ji mazauna ƙauyen.

Matar ƙanin Muhammadu Sani ce kawai ta tsira, in ji rahotanni, yayin da sauran mutum 12 da ke ciki suka mutu sakamakon tsananin zafi da wuta.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Zamfara ya tabbatar da harin, amma ya ce adadin waɗanda suka mutu 11 ne, in ji jaridar Daily Trust.

Daga baya dai an binne ‘yan gida ɗayan a ranar Lahadi, in ji rahotanni.

Harin na Gidan Taba shi ne na baya bayan nan a cikin jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Maradun na jihar Zamfara.

A makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a Gidan Kano a kan babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto.

Jami’an na tafiya ne a cikin wata motar bas mai ɗaukar mutum 18 ta hukumar sufuri ta jihar Zamfara domin samar da tsaro a lokacin sake zaɓen fid da gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Zamfara ta Arewa. Jami’ai biyar aka kashe a kwanton ɓaunar.