Nijeriya

‘Yanbindiga sun kashe mutum tara a jihar Filaton Nijeriya

‘Yan bindigar da ba a san su wane ne ba sun buɗe wuta bayan sun isa yankin Barkin Ladi, in ji rahotannin. An ji wa wasu ciwo a harin.

Newstimehub

Newstimehub

21 Sep, 2026

57350c2d 1b5b 4b60 9352 c1033bad97ee 1789988399914

Wani harin ‘yanbindiga ya kashe mutum tara a jihar Filato ta Nijeriya tsakanin daren ranar Asabar da safiyar Lahadi, in ji rahotannin kafafen watsa labarai na cikin ƙasar.

‘Yan bindigar da ba a san su waye ba sun buɗe wuta bayan sun isa yankin Barkin Ladi, in ji rahotannin. An ji wa wasu ciwo a harin.

A nata ɓangaren riundunar sojin Nijeriya ta bayyana a wata sanarwa cewa ta ƙaddamar da samame kan ‘yanbindiga a yankunan Shere da Gwafan da kuma Tsaunukan Maza a jihar.

Sha ɗaya daga cikin ‘yanbindigar ne aka kama a lokacin samamen, in ji sanarwar.

‘Yanbindiga suna ƙaddamar da hare-hare daga lokaci zuwa lokaci a Jihar Filato.

Kimanin mutum goma ne aka kashe a hare-haren da ‘yanbindigar suka ƙaddamar a jihar a cikin watan Yuli, in ji rahotanni.

Nijeriya ta daɗe tana fuskantar hare-haren ‘yanbindiga a sassan daban-daban na ƙasar da kuma hare-haren ‘yanta’addan Boko Haram.