Nijeriya

‘Yanta’addan ISWAP sun kashe sojojin Nijeriya 14 a hare-hare biyu

Mayaƙan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojin Nijeriya a garin Ngoshe, da ke ƙaramar hukumar Gwoza , inda suka kashe aƙalla sojoji tara da kuma wani limamin gari, kamar yadda majiyoyin soji uku suka bayyana da yammacin Laraba.

Newstimehub

Newstimehub

5 Mar, 2026

3a6c059400070d2397e1d765decaf0194139de0ecbc1f86d6605e4533dce4288

‘Yan ta’addan ISWAP sun kashe sojojin Nijeriya 14 tare da jikkata wasu a hare-hare da suka kai sansanonin soji biyu a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ranar Talata da daddare, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hakan na faruwa ne yayin da ‘yanbindigar ke zafafa kai hare-haren a sansanonin sojin ƙasar.

Mayaƙan ISWAP sun kai hari sansanin sojin Nijeriya a garin Ngoshe, da ke ƙaramar hukumar Gwoza, inda suka kashe aƙalla sojoji tara da kuma wani limamin gari, kamar yadda majiyoyin soji uku suka bayyana da yammacin Laraba.

Maharan, waɗanda suka tilasta wa dakarun ja da baya daga sansaninsu, sun ƙwace bindigogi da harsasai sannan suka yi awon-gaba da wasu mata da ba a san adadinsu ba, kamar yadda majiyoyin da ba su yarda a ambaci sunayensu ba saboda ba da su da ikon magana da kafofin watsa labarai a hukumance suka bayyana.

Kazalika ‘yanta’adda sun kai hari kan wani sansanin soji a Pulka, da ke arewaci a yankin Gwoza, inda suka kashe sojoji biyar, ciki har da wani kwamanda, kamar yadda wasu majiyoyi biyu da ke sane da harin suka bayyana.

Dakarun da suka jikkata kuma an kai su birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin samun kulawa.

‘Yanta’adda suna ƙaddamar da hare-hare domin rarraba hankulan sojin Nijeriya da kuma taƙaita ikonta na iya ƙaro ɗaukin sojoji da kayayyakin yaƙi.

Rundunar sojin Nijeriya ba ta amsa buƙatar yin toskaci game da lamarin ba.

 Sojin Nijeriya tana dannawa cikin wuraren da ‘yan ta’ddan suke da iko a arewa maso gabashin Nijeriya a cikin wannan shekarar a wani ɓangare na sabunta farmaƙi kan ƙungiyoyin ‘yanta’adda.

Amma duk da jerin farmaƙin, ISWAP da Boko Haram sun ci gaba da kai manyan hare-hare, inda suke amfani da yanayin wuraren da ke da wahalar shiga da kan iyakoki da babu tsaro sosai a wasu sasssan arewa maso gabashin Nijeriya wajen aika-aikarsu.

 Kawo yanzu dai Jihar Borno ce tsakiyar hare-haren ta’addancin da ya kai shekara 17 waɗanda suka kashe dubban mutane tare da raba mutum miliyan biyu da muhallansu, in ji ƙungiyoyin ba da agaji.