A wani mataki da ya janyo hankalin al’umma, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa za ta gurfanar da wasu daga cikin jami’anta a gaban kotun soji, bayan kammala bincike kan zargin cewa sun shiga yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daraktan Watsa Labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce an kammala cikakken bincike kan sojoji 16 da aka kama tun watan Oktoban 2025 bisa zargin rashin ɗa’a da karya dokokin aiki. Rahoton binciken ya nuna cewa wasu daga cikinsu sun shiga yunkurin da ya saba wa dokokin soji da kundin tsarin mulkin ƙasa.
Rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotun soji, domin fuskantar hukunci bisa tanade-tanaden dokokin soja da na ƙasa, a wani yunkuri na tabbatar da ladabtarwa da kiyaye tsarin mulki a cikin rundunar.














