Farashin ƙwallon kaɗanya, wanda ake amfani da shi a kayan kwalliya da kuma kayan zaƙi, ya fadi a Nijeriya bayan gwamnatin ƙasar ta shiga sahun sauran ƙasashen Yammacin Afirka wajen hana fitar da shi ƙasashen waje.
A cewar Rildwan Bello, Shugaban kamfanin Vestance da ke Legas, wanda ke bibiyar farashin kayayyakin gona ya ce farashin ya ragu zuwa Naira 800,000 ($521) kan kowane ton a ranar Alhamis, wanda ya yi ƙasa da kashi 33 cikin ɗari daga farashin da aka sayar kwanaki kaɗan da suka gabata.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa an sanya haramcin watanni shida ne domin “tabbatar da isasshen kaya ga masu sarrafa shi a cikin gida da samar da ayyukan yi, da kuma kare harkar da mata ne suka fi rinjaye wajen tattara shi da kashi 95 cikin 100.”
Sai dai Bello ya ce, duk da cewa manufar gwamnatin ƙasar mai kyau ce, hakan zai haifar da matsalolin kuɗi ga manyan ‘yan kasuwa da ke fitar da shi, waɗanda yanzu za su iya samun matsala musamman ga waɗanda suka samu kwangilar fitar da shi.
“Fitar da shi waje ce ke sa kasuwar ta yi armashi. Abin da ake buƙata a cikin gida bai kai kai adadin wanda ake samu ba,” in ji shi.














