Afirka

UNGA 80: Nijar ta ce dole Faransa ta ‘ɗauki alhakin laifukan da ta yi’ mata tun daga shekarar 1899

Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, a jawabinsa a Babban Taron MDD, ya zargi Faransa da “haddasa rashin zaman lafiya” a ƙasashen Sahel inda take ɗaukar nauyin “‘yan ta’adda” tare da tunzura rikici a ƙasarsa da maƙotanta.

Newstimehub

Newstimehub

28 Sep, 2025

b7005a5867bcc55ccc6015bb1de30f264b0e5dc55f272c49944f7200bc69e0b0

Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, ya caccaki Faransa kan yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan da suka aikata” a Nijar tun daga shekarar 1899.

“Tun lokacin da muka fatattaki sojojinsu daga [Nijar] a 2023, gwamnatin Faransa take kitsa wani shiri na ƙarƙashin ƙasa domin wargaza ƙasata,” in ji Ali Lamine Zeine a jawabin da ya gabatar a gaban Babban Taron MDD [UNGA] ranar Asabar.

Kazalika ya zargi Faransa da “bayar da horo da kuɗi da kuma makamai ga ‘yan ta’adda” tare da yunƙurin haifar da “rikicin ƙabilanci” a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel.

Firaministan na Nijar ya ƙara da cewa mahukunta a Paris sun ƙaddamar da wani kamfe na watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata ƙasarsa da shugabanninta da hukumominta a idanun duniya.

Lamine Zeine ya shaida wa taron UNGA cewa Faransa tana rura wutar rikicin “siyasa tsakanin ƙasata da kuma wasu maƙotanmu,” inda ya ƙara da cewa Faransa tana hana Nijar aiwatar da ayyukan ci-gaba tare da hana hukumomin kuɗinta sakat.

“Wannan ya haɗa da ƙiyayyar da Faransa take nuna mana wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba ta hanyar hana masu son zuba jari na ƙasashen duniya irin su ADB da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a ƙasarmu,” in ji shi.