Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gabatar da ƙara a gaban Kotun Jiha ta Kwara da ke Ilorin kan wasu ’yan ƙasar Indiya uku da kuma wani ɗan Najeriya, a ranar Laraba 17 ga Disamba, 2025.
An gurfanar da mutanen ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi haɗa baki da aikata laifin zamba ta hanyar cin amana, laifukan da ake zargin sun faru ne a lokacin da suke aiki a Kamfanin KAM Steel daga watan Nuwamba 2024 zuwa Satumba 2025. EFCC ta bayyana wannan bayani ne ta kafar sada zumunta ta X. Lokacin da aka karanta wa waɗanda ake zargi ƙarar, sun musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsu da su.
Bayan hakan, lauyan hukumar EFCC, Cosmas Ugwu, ya buƙaci kotu ta ba da umarnin tsare su a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a fara shari’a. Sai dai lauyoyin masu ƙara sun roƙi kotu da ta ba su beli, suna mai cewa laifukan da ake tuhumarsu da su na daga cikin waɗanda doka ta amince da bayar da beli.
A nasa martanin, lauyan EFCC ya jaddada cewa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma ba ’yan ƙasar Najeriya ba ne, kuma akwai yiwuwar su tsere idan aka ba su beli, don haka ya nemi kotu ta gaggauta sauraron shari’ar.
Bayan jin dukkan hujjojin ɓangarorin biyu, Alƙalin kotun, Sulaiman Akanbi, ya ɗage shari’ar zuwa ranar Juma’a 19 ga Disamba, 2025.














