Amurka Nijeriya Siyasa

Amurka Ta Dakatar da Ba ‘Yan Nijeriya Biza Daga Janairu 2026

Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da nau’ikan biza da suka haɗa da B-1/B-2 (na kasuwanci da yawon shakatawa), F, M, J (na ɗalibai da musayar maziyarta), da kuma bizar ‘yan gudun hijira. Nijeriya na cikin ƙasashe 19 da wannan mataki ya shafa, ciki har da Angola, Cuba, Venezuela, Senegal da wasu ƙasashe.

Sai dai gwamnatin Amurka ta ware wasu rukuni daga wannan mataki, ciki har da masu fasfon wata ƙasa daban, mazauna na dindindin bisa ƙa’ida, mahalarta wasanni na kasa da kasa, da kuma wasu rukunin ‘yan tsiraru daga Iran.

Newstimehub

Newstimehub

23 Dec, 2025

055fb5f7d1dbb021798ed59b6af54a6dae8ca19b34ab0bb3a9effc3e6af89ef9 e1766503431339

‘Yan Nijeriya da dama sun wayi gari da labarin da ya tayar da hankula, bayan da gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza ga ‘yan ƙasar daga ranar 1 ga Janairun 2026. Sanarwar, wadda Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar, ta nuna cewa matakin zai shafi nau’ikan biza da dama, lamarin da ka iya shafar ɗalibai, matafiya da masu neman dama a ƙasar Amurka.

Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da nau’ikan biza da suka haɗa da B-1/B-2 (na kasuwanci da yawon shakatawa), F, M, J (na ɗalibai da musayar maziyarta), da kuma bizar ‘yan gudun hijira. Nijeriya na cikin ƙasashe 19 da wannan mataki ya shafa, ciki har da Angola, Cuba, Venezuela, Senegal da wasu ƙasashe.

Sai dai gwamnatin Amurka ta ware wasu rukuni daga wannan mataki, ciki har da masu fasfon wata ƙasa daban, mazauna na dindindin bisa ƙa’ida, mahalarta wasanni na kasa da kasa, da kuma wasu rukunin ‘yan tsiraru daga Iran.

Majiyar Labari: Trt Hausa