Afirka Wasanni

Ko Tanzania Za Ta Iya Karya Tarihin Rashin Nasara a Gaban Nijeriya a AFCON 2025?

Nijeriya da Tanzania za su fafata a wasansu na farko na AFCON 2025 a Maroko, inda Tanzania ke fatan karya tarihin rashin nasara da take da shi a gaban Super Eagles.

Newstimehub

Newstimehub

23 Dec, 2025

2025 10 13t193217z 282649812 up1elad1i9rno rtrmadp 3 soccer worldcup nga ben preview e1766515216619

Idan aka duba tarihin haduwar ƙungiyoyin biyu, tambayar da ke yawo a zukatan masoya ƙwallon ƙafa ita ce: shin Tanzania za ta iya karya lagon da ta kasa karya tsawon shekaru a gaban Nijeriya? A yau Talata ne dai tawagogin ƙwallon ƙafa na Nijeriya da Tanzania za su fafata a wasan farko na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2025 da ke gudana a Maroko, wasa da ke ɗauke da muhimmanci ga ƙasashen biyu, musamman Tanzania.

Wasan na Rukunin C shi ne karo na huɗu da tawagar Tanzania, wadda aka fi sani da Taifa Stars, ke halartar gasar AFCON a tarihinta. A baya, Tanzania ta halarci gasar a shekarun 1980, 2019 da 2024, amma ba ta taɓa samun nasara ba a kowace daga cikin waɗannan halartar, inda aka fitar da ita tun a matakin rukuni a duk lokutan.

Idan aka koma tarihin karawa tsakaninta da Nijeriya, alkaluman ba su yi wa Tanzania dadi ba. A wasanni bakwai da ƙasashen biyu suka buga a tsakaninsu, Nijeriya ta yi nasara a wasanni huɗu, yayin da aka tashi canjaras sau uku. Har yanzu Tanzania ba ta taɓa doke Nijeriya ba ko sau ɗaya.

Duk da wannan tarihin, jami’an Tanzania sun nuna ƙwarin gwiwa. Mataimakin Ministan Harkokin Labarai, Al’adu, Nishaɗi da Wasanni na Tanzania, Paul Makonda, ya bayyana hakan bayan ganawarsa da ‘yan wasan Taifa Stars a Barcelo Convention Center da ke birnin Fes, Maroko, inda tawagar ta kafa sansanin shirinta.

“Duk da yanayin da muke ciki mai wahala, mun zaɓi nasara. Mun san ‘yan Nijeriya, mun riga mun buga da ‘yan Uganda kuma mun san su sosai, har ma mun san ‘yan Tunisia,” in ji Makonda, yana nuna kwarin gwiwar cewa tawagarsa za ta iya fuskantar ƙalubalen.

A yanzu haka, fatan al’ummar Tanzania shi ne ganin Taifa Stars sun yi abin a yaba a wannan muhimmin wasan Rukunin C, yayin da ake sa ido kan sakamakon wasan da zai gudana tsakanin Uganda da Tunisia.

Wannan wasa na da matuƙar muhimmanci ga Tanzania, musamman ganin cewa ƙasar za ta kasance mai masaukin baki tare da Kenya da Uganda a gasar AFCON ta 2027. Tawagar Nijeriya, Super Eagles, za ta fafata da Taifa Stars a yau 23 ga Disamba 2025 a gasar AFCON 2025, a wasan da ke iya zama tarihi ga ɓangare ɗaya daga cikin su.

Majiyar Labari: Trt Hausa