Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel (AES), inda ya yi alkawarin ɗaukar manyan matakai bayan kafa rundunar haɗin gwiwa domin yaƙi da ta’addanci.
Shugaban Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré ya karɓi shugabancin ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Sahel (AES) da ta ƙunshi Mali, Burkina Faso da Nijar, yana mai bayyana cewa bayan kaddamar da rundunar sojojin haɗin gwiwa, wajibi ne a aiwatar da manyan ayyuka a kwanaki masu zuwa domin tinkarar matsalolin tsaro da ta’addanci da suka addabi yankin.
Traoré bai yi cikakken bayani kan waɗannan matakai ba a jawabinsa na farko bayan nadin, amma ya jaddada aniyar ƙungiyar na ƙarfafa tsaro da farfaɗo da tattalin arziki. Ƙungiyar AES, wadda aka kafa a shekarar 2023, ta ƙunshi ƙasashe uku da ke ƙarƙashin mulkin soji, kuma a wannan shekara suka fice daga ECOWAS.
Yankin Sahel na daga cikin wuraren da suka fi fuskantar ta’addanci a duniya, inda ƙungiyoyin masu alaƙa da al-Qaeda da Daesh ke ci gaba da kai hare-hare. A wani taro da shugabannin ƙasashen suka gudanar, sun amince da ƙarfafa haɗin kai, tare da ɗaukar matakin korar sojojin ƙasashen waje, musamman na Faransa da Amurka.
Ƙungiyar AES, wadda ke da yawan jama’a kusan miliyan 78, na neman cikakken ’yancin kai da haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, tare da kiran a aiwatar da manyan ayyuka na bai ɗaya domin murƙushe ’yan ta’adda a yankin.














