Hukumomin tsaro a Ghana sun cafke mutane 50 da ake zargi da aikata laifukan intanet, a wani samame da aka kai da tsakar dare wanda ya sake jawo hankalin jama’a kan yawaitar ayyukan zamba ta yanar gizo a ƙasar.
Ministan sadarwa na Ghana, Sam George, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 46 da mata 3, kuma ana kyautata zaton yawancinsu ’yan Najeriya ne. Ya ce tuni aka fara bincike a kansu.
An kama mutanen ne bayan wani samame da jami’an yaƙi da laifukan intanet suka kai a yankin Dawhenya tare da haɗin gwiwar ’yansandan yankin. Ana zarginsu da laifuka kamar zamba, zuba jari na jabu, da kasuwancin zinare na ƙarya.
Wannan kamen na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da hukumomin Ghana suka kama wasu ’yan Najeriya 32 da ake zargi da irin waɗannan laifuka a wani ɓangare na ƙasar.














