Fiye da mutane 200, ciki har da mata da ƙananan yara, sun mutu sakamakon hare-haren kabilanci da ake zargin dakarun RSF sun kai a wasu sassan yankin Darfur na ƙasar Sudan, a cewar likitoci.
Rahotanni daga waɗanda suka tsira sun nuna cewa an kai hare-haren ne a Ambro da Abu Qamra a Arewa Darfur, da kuma Sirba a Yamma Darfur, inda aka rika kai wa fararen hula hari bisa asalin kabilarsu. Likitocin sun ce wannan lamari ya saba wa dokokin jin ƙai da kare haƙƙin ɗan Adam na duniya.
Hare-haren sun zo ne yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, rikicin da ya tilasta wa miliyoyin mutane barin muhallansu tun daga shekarar 2023.














