Sabbin bayanai daga Abuja sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa za a fara aiwatar da sabbin dokokin haraji a ranar 1 ga Janairu kamar yadda aka tsara, duk da korafe-korafe daga ‘yan adawa da kungiyoyin matsin lamba. Ya ce dokokin ba don ƙara haraji aka tsara su ba, sai dai don daidaita tsarin kudi, haɓaka haɗin gwiwa, da kafa tsarin haraji mai gaskiya da dorewa a Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa waɗannan sauye-sauyen haraji suna da muhimmanci matuƙa ga makomar tattalin arziƙin ƙasar, yana kuma roƙon ‘yan Najeriya su ba da haɗin kai. Duk da haka, rikici ya ci gaba bayan dan majalisa Abdussamad Dasuki ya yi zargin cewa abin da aka buga a gazette bai yi daidai da abin da majalisa ta amince da shi ba. Wannan ya sa shugabannin adawa irin su Atiku Abubakar da Peter Obi, da NBA, suka nemi a dakatar da aiwatarwa har sai an gama bincike.
Sabbin dokokin da aka rattaba musu hannu sun haɗa da Nigeria Tax Act, Nigeria Tax Administration Act, Nigeria Revenue Service Act, da Joint Revenue Board Act, inda za a gudanar da su ƙarƙashin hukuma guda.














