An fara aiwatar da sabbin dokokin haraji da aka amince da su a Najeriya, yayin da Majalisar Ɗinkin Ƙasa ta ƙara ɗaukar matakai na buɗaɗɗen aiki domin ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin dokoki. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara da damuwa daga al’umma kan sauye-sauyen haraji.
Domin amsa irin waɗannan damuwa, Majalisar ta bayar da umarnin fitar da Certified True Copies (CTCs) na dokokin harajin da aka daidaita, waɗanda ’yan majalisa suka amince da su kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu ya zama doka.
Magatakardar Majalisar Ɗinkin Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa ’yan Najeriya damar samun sahihan takardun doka kai tsaye, tare da kawar da shakku kan inganci da sahihancin sabbin dokokin haraji.
A cikin wata sanarwa, Ogunlana ya ce jama’a yanzu za su iya samun dokokin da Shugaban Ƙasa ya rattaba hannu a kansu domin yin nazari da tantancewa da kansu. Ya jaddada cewa wannan na nuna ƙudirin majalisa na gaskiya da ɗaukar alhaki, musamman a lokacin da ake samun muhawara mai zafi kan dokokin haraji.
Ya ƙara da cewa wannan umarni ya biyo bayan zarge-zargen da ke cewa akwai sabani tsakanin Votes and Proceedings na Majalisar da kuma dokokin haraji da aka wallafa a cikin jaridar hukuma (gazette).
Duk da yawan ce-ce-ku-ce a bainar jama’a, Ogunlana ya bayyana cewa ƙalilan ne kawai suka nemi CTCs a hukumance zuwa yanzu. Ya tabbatar da cewa dukkan buƙatun da aka shigar an bi su bisa ka’ida, tare da bayyana cewa duk mai sha’awa na iya ci gaba da nema ta Ofishin Magatakardar Majalisa, bayan biyan kuɗaɗen da doka ta tanada.
Magatakardar ya kuma bayyana cewa ofishinsa na aiki tare da Federal Government Printing Press (FGPP) domin tabbatar da gaggawar wallafa dokokin da aka tabbatar, inda ya ce ana sa ran fitowar su a jaridar hukuma tun daga jiya.
Ya ƙara da cewa, duk da cewa Magatakarda ne ke fara aikin gazette, aikin bugawa da wallafawa na hannun FGPP ne bisa doka.
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai, Bullah Audu Bi-Allah, ya sanya wa hannu a madadinsa, Ogunlana ya sanar da sabbin matakai da aka ɗauka domin kauce wa rikice-rikice makamancin haka nan gaba.
Daga yanzu, duk wasu dokoki da za a kai wa Shugaban Ƙasa domin amincewa, za su rika wucewa ne ta hannun Jami’an Hulɗa da Fadar Shugaban Ƙasa, kuma ba za a wallafa kowace doka ba sai dai idan Magatakardar Majalisa ko wakilinsa da aka amince da shi ne ya fara da buƙatar hakan.
A ƙarshe, Ogunlana ya jaddada cewa Majalisar Ɗinkin Ƙasa na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ƙwarewa a dukkan ayyukanta na kundin tsarin mulki.














