Hukumar Kula da Fansho ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta biya sama da naira biliyan 12.6 a matsayin haƙƙoƙin ritaya ga tsoffin ma’aikata fiye da 5,000 daga 2024 zuwa Janairu 2026, a wani mataki da ke nuna ƙudirin gwamnatin jihar na kula da walwalar ma’aikata.
Shugaban Ma’aikatan Jihar, Alhaji Muhammad Dagaceri, ya bayyana hakan a yayin kaddamar da rabon naira biliyan 1.5 ga tsoffin ma’aikata 592 a hedikwatar Hukumar Fansho da ke Dutse. Ya ce a shekarar 2024, Gwamna Umar Namadi ya amince da sakin naira biliyan 5.42 ga tsoffin ma’aikata 2,033, yayin da a 2025 aka biya naira biliyan 5.68 ga wasu 2,211.
A Janairu 2026 kuma, an sake raba naira biliyan 1.51 ga tsoffin ma’aikata 592 daga kananan hukumomi da hukumomin ilimi. Dagaceri ya ce wannan na nuna aniyar gwamnan na biyan dukkan bashin fansho tare da inganta walwalar ma’aikatan gwamnati.
Sakataren Hukumar Fansho, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya ƙara da cewa kudin sun haɗa da haƙƙin ritaya, alawus na mutuwa, da ragowar fanshon waɗanda suka rasu suna kan aiki, ga ma’aikatan jiha, kananan hukumomi da hukumomin ilimi.
Hukumar ta ce ta tabbatar da cewa dukkan biyan kuɗaɗe suna tafiya yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa babu wani tsohon ma’aikaci ko iyalinsa da aka bari a baya.
- Majiyar Labari: TVC NEWS














