Shugaban Ghana, John Mahama, ya bayyana shirin gina sabbin gidaje ga ’yan sanda da sojoji, a wani yunƙuri na inganta matsuguni da walwalar jami’an tsaro a ƙasar. Shirin ya shafi rundunar ’yan sanda, gidajen yari, hukumar kashe gobara da kuma sojojin Ghana.
Mahama ya ce yarjejeniyar ta samu ne a lokacin ziyararsa zuwa Singapore a 2025, inda aka kulla fahimta da wani kamfani domin kafa masana’antar gidaje na zamani (prefabricated housing) a Ghana. A cewarsa, aikin farko na kamfanin shi ne gina ɗakin kwanan ɗalibai mai ɗaukar mutum 10,000 a Jami’ar Ghana.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron ƙarshen shekara na rundunar ’yan sanda (WASSA) a Accra, inda ya ce an riga an ba kamfanin aikin gina gidaje a barikin ’yan sanda, gidajen yari, hukumar kashe gobara da sojoji. Ya bukaci hukumomin tsaro da su fara ware filayensu domin fara aikin.
Mahama ya ce shirin na cikin ajandar “Big Push” kuma zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar jami’an tsaro. Ya kuma yaba wa rundunar ’yan sanda bisa yadda ta tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti, yana cewa hakan ya bai wa ’yan ƙasa da baƙi damar gudanar da bukukuwa cikin kwanciyar hankali.














