Tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Mallam Abubakar Malami (SAN), na fuskantar sabon bincike daga Hukumar DSS kan makamai da harsasai da aka gano a gidansa da ke Birnin Kebbi.
Rahoton The Nation ya ce jami’an EFCC ne suka gano makaman yayin bincike, amma suka miƙa su ga DSS saboda rashin hurumin binciken mallakar makamai. An ce adadin makaman ya kai matakin da ya janyo cikakken bincike.
A makon da ya gabata, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da beli ga Malami, matarsa da ɗansa kan kuɗi Naira miliyan 500, sai dai har yanzu yana tsare a gidan gyaran hali na Kuje sakamakon kasa cika sharuddan belin.
Wasu majiyoyi sun ce Malami na jinkirta cika belin ne domin kauce wa gayyatar DSS. EFCC ta kuma karyata rahotannin da ke yawo cewa ya koma Kebbi.
A gefe guda, kotu ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da Malami da ’ya’yansa, waɗanda darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 213, tare da ba su wa’adin kwanaki 14 su kare kansu.














