Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta sanar da cewa hare-haren sama da ta kai a yankunan Azir da Musarram na jihar Borno sun yi sanadin kashe fiye da ’yan ta’adda 40 tare da tarwatsa shirinsu na kai farmaki kan al’ummomin fararen hula.
Hare-haren, da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Janairu a ƙarƙashin Operation Hadin Kai, sun biyo bayan sahihan bayanan leken asiri da suka nuna taruwar ’yan ta’adda a kan kwale-kwale da kuma ƙarƙashin wasu bishiyoyi domin shirin kai hari a yankunan Baga da Fish Dam.
Kakakin NAF, Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai farmakin ne bayan gano motsinsu, inda jiragen sama suka hallaka da dama daga cikinsu tare da tarwatsa wuraren da suke taruwa.
Binciken bayan harin ya tabbatar da raguwar barazanar tsaro da kuma dawowar kwanciyar hankali, yayin da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da bai wa sojojin ƙasa cikakken goyon bayan sama domin murƙushe ’yan ta’adda gaba ɗaya.














