Nijeriya

Dorinar Ruwa Sun Lalata Gonaki a Gombe, Manoma Sun Fadi Asara Mai Tsanani

Dorinar ruwa sun yi barna a gonakin Hinna a Gombe, sun jawo wa manoma asarar miliyoyin naira tare da tayar da hankula game da tsaron abinci.

Newstimehub

Newstimehub

22 Jan, 2026

0a9089232dd985d3dbf7361063471250e31997c210795dd6814c4c566a12ca10

A daren Talata, dorinar ruwa da suka fito daga wani kogi a ƙauyen Hinna, ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba a Jihar Gombe, sun mamaye gonaki da dama inda suka lalata amfanin gona da manoma ke shirin girba, lamarin da ya jefa su cikin baƙin ciki da fargabar rasa abin dogaro.

An kiyasta cewa gonaki 17, masu fadin kusan hekta 14, sun lalace baki ɗaya, tare da asarar kuɗi da ta kai kimanin naira miliyan bakwai, abin da ke barazana ga rayuwar manoman da kuma tsaron abinci a yankin.

Majiyar Labari: TRT HAUSA