Gwamnatin Ghana ta samu wani abin ƙarfafawa a fagen yaƙi da talauci, bayan wani sabon rahoto ya nuna cewa adadin mutanen da ke rayuwa cikin matsanancin talauci yana raguwa a ƙasar. Duk da cewa har yanzu akwai gibi mai yawa a rabon kuɗaɗen shiga tsakanin al’umma, alkaluman baya-bayan nan sun nuna ci gaba mai kyau.
Rahoton Quarterly Multi-Dimensional Poverty Index (MPI) na Hukumar Ƙididdiga ta Ghana (GSS) ya bayyana cewa cikin watanni uku kacal, daga Yuli zuwa Satumba 2025, fiye da mutane 360,000 sun fita daga kangin matsanancin talauci. Haka kuma, tsakanin Afrilu 2024 zuwa Maris 2025, sama da mutane 950,000 sun samu sauƙin rayuwa, inda kaso na talauci ya ragu daga 24.9% a 2024 zuwa 21.9% a 2025.
Adadin mutanen da ke rayuwa cikin talauci gaba ɗaya ya ragu daga miliyan 8.1 a Yuni 2024 zuwa miliyan 7.2 a ƙarshen Satumba 2025, abin da ke nuna cewa shirye-shiryen gwamnati da tallafin jin ƙai suna fara haifar da sakamako.
Rahoton MPI bai tsaya kan kuɗin shiga kaɗai ba, yana kuma la’akari da:
Yanayin rayuwa
Kiwon lafiya
Ilimi
Aiki da sana’a
Ana ɗaukar iyali a matsayin matalauta idan ya kasa cika akalla kashi ɗaya cikin uku na waɗannan ma’aunai. A cewar GSS, kiwon lafiya da yanayin rayuwa su ne ke da tasiri mafi girma, suna ɗauke da kaso 76.9% na dukkan ma’aunin talauci, yayin da ilimi ke da 13.4%, sai aiki/sana’a da ke da 12.3%.














