Sabbin takardun da aka fitar game da Jeffrey Epstein sun jawo ce-ce-ku-ce bayan wani imel da ke ambaton Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya bayyana, lamarin da ya sa New Delhi ta yi kakkausar martani. A cewar rahoton Jerusalem Post, imel ɗin ya yi tsokaci kan ziyarar Modi ta shekarar 2017 zuwa Isra’ila, inda aka yi ikirarin da hukumomin Indiya suka ce ba shi da tushe balle makama.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Indiya ta ce abin da ya tabbata kawai shi ne ziyarar Modi zuwa Isra’ila, wadda aka rubuta a hukumance, tare da yin watsi da sauran kalaman a matsayin maganganun banza daga wani da aka yanke wa hukunci. Kakakin ma’aikatar ya ce babu wata hujja da ke nuna wata alaƙa ko shawarwari tsakanin Modi da Epstein, duk da cewa jam’iyyun adawa sun nemi karin bayani.
Takardun sun kuma nuna wata yarjejeniya ta dala miliyan 25 da Epstein ya kulla a 2015 da rukunin Rothschild ta hannun kamfaninsa Southern Trust Company Inc., domin bayar da ayyukan nazarin haɗari da amfani da wasu algoritim. Yarjejeniyar ta fayyace haɗin gwiwa kan wasu ayyuka na musamman, inda Rothschild za ta biya kudin a kan aikin da aka tsara.
A wani bangare, imel-iman sun nuna tattaunawa game da Somaliland, inda aka ambaci damar zuba jari a fannonin ruwa, harkokin kudi da masana’antar fim. Wannan ya zo ne yayin da matsayin Somaliland ya sake daukar hankalin duniya bayan sanarwar Isra’ila a karshen 2025 na amincewa da yankin, matakin da ya jawo suka daga yankin da kasashen duniya.
Majiyar Labari: TRT WORLD
















