Lafiya

Gaggawar Cizon Maciji: Muhimman Matakan Farko da Za Su Iya Ceton Rai

Mutuwar Ifunanya Nwangene ta sake jaddada cewa sanin agajin farko da gaggawar kai wanda maciji ya ciza asibiti na iya zama mabuɗin ceton rai.

Newstimehub

Newstimehub

2 Feb, 2026

Snake bite 510x340 1

Mutuwar fitacciyar mawaƙiyar Nijeriya, Ifunanya Nwangene, ta sake jawo hankalin jama’a kan muhimmancin shiri da gaggawa wajen fuskantar cizon maciji da kuma muhimmiyar rawar da agajin farko ke takawa kafin a kai marar lafiya asibiti. Nwangene, wadda take mawakiya soprano a ƙungiyar Amemuso Choir, ta rasu a ranar Asabar a Asibitin Gwamnati na Tarayya (FMC) da ke Abuja bayan ta samu cizon maciji, kamar yadda daraktan kiɗan ƙungiyar, Sam Ezugwu, ya tabbatar.

Bayan mutuwarta, an samu ce-ce-ku-ce kan ƙarancin maganin rigakafin guba (anti-venom) a asibitocin gwamnati. Sai dai FMC Jabi ta fitar da sanarwa inda ta ce an ba marigayiyar cikakken kulawar gaggawa, ciki har da maganin anti-venom, bayan da aka gano tana fama da matsananciyar illa ta gubar maciji mai tasiri kan jijiyoyi (neurotoxic). Asibitin ya ce duk da ƙoƙarin da aka yi, yanayinta ya ta’azzara kwatsam kafin a kaita dakin kulawa ta musamman (ICU).

Duk da bayanin asibitin, masana kiwon lafiya sun ce agajin farko a wurin da abin ya faru na da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗarin mutuwa. A lokuta da dama, mintuna na farko bayan cizo na iya zama bambanci tsakanin rai da mutuwa, musamman idan an san yadda za a kula da wanda aka ciza kafin kai shi asibiti.

Matakan Agajin Farko na Cizon Maciji (Mataki-mataki):

  • Kwantar da wanda aka ciza: A hana shi motsi domin rage yaduwar guba a jiki.

  • Ajiye sashen da aka ciza ƙasa ko daidai da zuciya: Kada a ɗaga shi sama.

  • Cire abubuwa masu matse jiki: Kamar zobba, agogo ko tufafi masu matsewa kusa da wurin cizon.

  • Tsaftace wurin a hankali: A wanke da ruwa da sabulu idan akwai, ba tare da matsa ƙarfi ba.

  • Daurewa da bandeji mai matsin lamba (idan zai yiwu): Musamman ga macizai masu guba ta jijiyoyi, a nade bandeji daga yatsu zuwa sama amma ba sosai har ya katse jini ba.

  • A gaggauta kai mara lafiyan asibiti: Kada a bata lokaci da magungunan gargajiya.

 

Majiyar Labari: TVC NEWS